Ƙungiyar kwadago a Najeriya ta yi watsi da batun ƙarin albashin da gwamnatin tarayya ta yi na wasu rukuni shida.



Kungiyar ta yi watsi da ƙarin tare da jaddada matsayarsu kan mafi karancin albashi naira 615,000.
A wata tattaunawa da mataimakin babban sakataren Christ Onyeka ya bayyanawa jaridar Daily Trust cewar batun bata lokaci ne kawai.
Sai dai har zuwa daren jiya da gwamnatin ta sanar da ƙarin kungiyar ba ta bayyana gamsuwa a kai ba.
Gwamnatin ta ce ta ƙarawa ma’aikatan albashin ne da kashi 25, da kuma kashi 35 ga wasu rukuni shida na ma’aikatan.
Tun tuni ƙungiyoyin kwadago ke kiraye-kiraye da a ƙara musu albashi ganin yadda cire tallafin man fetur ya taɓa al’amura da dama.