Ƙungiyar ƴan kasuwa a Najeriya ta bai wa hukumar samar da wuta a Najeriya mako guda da ta janye batun ƙarin wutar lantarki da ta yi.



Shugaban ƙungiyar Fetus Osifo ne ya bayyana haka yau Laraba wanda ya ce sam ƙarin bai dace da ƴan Najeriya ba a wannan lokaci.
Yayin da yake jawabi a yau da ake ranar ma’aikata ta duniya, Fetus Osifo ya buƙaci a mayar da tsohon farashin wutar maimakon karin kusan kashi 300 da aka yi a kwanan nan.
Gwamnatin ta ƙara farashin ne zuwa sama da naira 250 kan kowanne megawatt guda maimakon naira 66 da ake biya a baya.
Rukunin da ke kan tsarin band A ne aka yi wa ƙarin wanda gwamnatin ta ce su na samun wuta tsawon awanni 24 a kowacce rana.
Sai dai maganar ta ci karo da wata magana da ministan makamshi ya yi cewar, ba za a taba samun tsayayyar wuta a Najeriya ba har sai an kashe dala biliyna goma duk shekara tsawon shekara goma.
Haka ma mataimakin shugaban ƙasa Sanata Kashim Shettima ya ce ƙasa da kashi 20 na ƴan kasar ne ke morar lantarki yayi da fiye da rabin ƴan kasar ba sa ta’ammali da ita baki daya.