Gwamnatin Jihar Kano ta sake bayyana aniyarta na sake gudanar da auren Zaurawa a Jihar.

Babban Kwamandan hukumar Hisba na jihar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya tabbatar da hakan a jiya Laraba a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Jihar.

A cewar Daurawa auren zai hada da bangarori daban-daban a Jihar.

Daurawa ya kara da cewa daga cikin wadanda za su shiga cikin jerin auren na zaurawa ciki har da manema labarai.

Kwamadan ya ce za a bai’wa manema labarai gurbi guda 50 a yayin auren.

Daurawa ya ce daga cikin sauran mutanen da za su amfana da auren na zaurawa ciki har da wasu bangarorin ma’aikata da suka hada da alkalai, lauyoyi, ma’aikatan lafiya da sauransu a dukkan fadin Jihar.

Sannan Malaman Daurawa ya bayyana irin nasarorin da aka samu a lokacin da aka aurer da zaurawa 1,800 wanda ya gabata.

Har ila yau ya kara da cewa sakamakon nasarar da aka samu a auren ne ya sanya suka bujiro da shigo da wasu bangarorin cikin lamarin domin su ma su samu damar shiga cikin shirin.

Daurawa ya ce an samar da shirin auren zaurawa ne domin rage aikata ba dai-dai ba a cikin al’umma.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: