Hukumar jin dadin alhazai ta kasa NAHCON ta sanya ranar 15 ga watan Mayu a matsayin ranar da za ta fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Kasar Saudiyya domin gudanar da ibadar aikin hajjin bana.

Shugaban hukumar na Kasa Malam Jalal Arabi ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabin bude taron masu ruwa da tsaki na harkar Hajji da Umrah wanda aka gudanar a Abuja.
Malam Arabi ya ce maniyyar 65,500 ne za su gundanar da aikin Hajjin bana a fadin Kasar,inda ya ce za ayi jigilar su ne daga filayen jiragen sama 10 na fadin kasar.

Shugaban ya kara da cewa hukumar ta tsayar da matsayar cewa a yayin aikin Hajjin na bana dukkanin alhazan Najeriya za su fara yin kwanaki akalla hudu a Madina kafin a fara aikin Hajjin.

A cewar Arabi sun shirya taron masu ruwa da tsaki ne domin tattaunawa da su don tabbatar da gudanar da aikin Hajjin na bana cikin nasara.
Arabi ya kara da cewa yana da kyau duk masu ruwa da tsaki su hada kai domin ganin alhazai sun samu gogewar aikin hajji na bana a Kasar ta Saudiyya.