Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta ce wasu jami’an ‘yan sanda da magoya bayan tsohon gwamnan ne suka kawowa jami’an EFCC cikas a yayin da suka je kama Yahaya Bello a gidansa da ke Abuja.

 

Sama da sa’o’i 10 tsohon gwamnan ya kasa fita daga gidansa har sai da magajinsa Ahmed Usman Ododo ya kai masa dauki, wanda kuma ake zargin ya taimaka wa Bello ya tsere.

 

EFCC ta ayyana Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo, inda ita ma hukumar DSS ta saka sunan shi a jerin wadanda za ta sakawa ido.

 

A baya an ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawar na shirin gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kuliya bisa zarge-zarge 19.

 

Zarge-zargen sun hada da halasta kudaden haram, cin amana, da karkatar da wasu kudade da suka kai Naira biliyan 80.2.

 

A halin da ake ciki, Ola Olukoyode, ya sha alwashin ajiye mukaminsa na shugaban hukumar EFCC idan har ba zai iya gurfanar da Yahaya Bello a gaban kuliya ba.

 

Olukoyode ya kara da cewa shugabancinsa za ta tabbatar da cewa duk wadanda suka kawo wa hukumar cikas a hukunta Bello sun fuskanci fushin doka.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: