Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta tabbatar da kama wata tankar mai da ake kokarin karkatarwa daga jihar Kano zuwa Katsina.

 

A sakon da jami’in hulda da jama’a na hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi ya aikewa manema labarai an gano tankar na dauke da litar mai 20,000.

 

Ya ce kwarya-kwaryar bincikensu ya gano cewa asalin man an turo shi ne zuwa gidajen man da ke Kano, amma aka samu wasu bata-gari na kokarin fitar da shi.

 

Hukumar tsaron farar hula ta NSCDC a Kano ta ce ta fara binciken wadanda ake zargi da kokarin safarar tankar mai daga jihar Kano zuwa Katsina.

 

Kakakin hukumar, Ibrahim Idris Abdullahi ne ya tabbatar da hakan.

 

Ya ce an kama tankar man ne a titin Ibrahim Taiwo road ta na kokarin fita zuwa wasu sassan Katsina.

 

Kakakin ya ce za a mayar da fetur din zuwa gidan man da aka dauko saboda da su domin ci gaba da sayarwa jama’a.

 

Ibrahim Idris Abdullahi ya ce ba za su yi kasa a gwiwa na wajen hukunta wadanda aka kama da zarar sun kammala bincike.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: