Kungiyar masana harkokin ma’aikatan Najeriya (NECA) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya kan yin gaggawa wurin kammala shirye-shiryen karin albashi.

Kungiyar ta ce jinkirin zai kara haifar da kokonto da rashin yarda tsakanin ma’aikata da gwamnati.


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kungiyar ne, Adewale Smart Oyerinde ya bayyana haka ga manema labarai.
Mista Oyerinde ya kara da cewa jinkirin da gwamnatin ke yi ya kawo rashin fahimta tsakanin kungiyar kwadago da gwamnonin jihohi.
Ya kuma bayyana cewa zaman da kwamitin karin albashin ya yi na karshe ya kai sama da wata daya amma har yanzu ba a ji wani bayani ba.
Shugaban kungiyar ya koka kan sabanin da aka samu tsakanin kungiyar kwadago da gwamnonin jihohi kan biyan N615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Sai dai ya yi kira ga dukkan bangarorin da su kai zuciya nesa da kuma jira kwamitin karin albashi na kasa ya fitar da nasa sakamakon
Duk da haka, ya kara da cewa dole ne karin albashin ya lura da irin nauyin da ke kan ma’aikata da kuma halin da ake ciki na tattalin arziki.