Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya umarci al’ummar musulmi da su fara duba jaririn watan Zulkida daga yau Laraba.

 

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin addinin Musulunci na masarautar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar a yau Laraba a Jihar Sokoto.

 

Sarkin ya bukaci al’umma da su kai rahotan ganin watan ga hakimin yankinsu domin isar da sakon ga Sarkin Musulmi.

 

Sanarwan ta kara da cewa bayar da tabbacin ganin watan hakan ne zai tabbatar da gobe Alhamis a matsayin 1 ga watan Zulkida na shekarar 1445.

 

Ya ce idan ba a ga watan a yau Laraba ba Juma’a ce za ta kasance daya ga watan Zulkida.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: