Rundunar yansandan jihar kano tayi holan wasu da ake zargin su da ayyukan Ta’addanci da garkuwa da mutane, tare da barayin motoci daban daban.

Tun a shekarun baya An samu yawaitar samun rahotan sace sace yara a unguwanni daban daban da suka hada da sauna kawaji, Yan kaba, hotoro, dakata to amma wannan lamarin yazo karshe.
Sakamakon irin Kokarin da jami’an yan sanda suke dan ganin ta kawo karshen Ta’addanci da sace sace.a fadin jihar kano.
Cikin Wayanda akayi holan su a Shelikwatar Yan sanda dake Bompai,
Sun hada da wani mai suna Mai suna Paul Owne dan shekaru 38 a unguwar dakata, da wata Mercy Paul, Emanuel Igwe, Ebere, lousa duru da Monica Oracha,
Dukkannin su da laifin sace yara kanan yara masu kanan shekaru da basu wuce shekaru 10 a duniya ba.

Kwamishinan Yan sandan jihar Kano CP Ahmad Ilyasu ya bayyana cewa zai kawo karshen aikin Ta’addanci garkuwa da mutane, da ma sace sacen motoci, duk a Kokarin Rundunar yansanda ta Kokarin jami’ai na musamman da ake Kira Operation Puff Adder.

Yaran da aka sace su a unguwannin Yan kaba, kwanar jaba, hotoro da dakata Quarters,
Dukkannin su yanU basa jin hausa sakamakon an kaisu jihohin Kudu.
Daga karshe CP Ahmad Ilyasu ya yaba wa yan jaridu da masa Yan kungiyar sintiri yadda suke bada gudunmawa don dakile Kokarin Yan Ta’adda a fadin jihar Kano.
Ya Kuma yi Kira da masu amfani da kafafen sada zumunta da su guji yada labaran karya da zai tada hankulan jama’a.
An ceto yara 8 da masu garkuwa da su 6. Sai Kuma kwato motoci 30 da aka sace su.