Aƙalla mutane 11 ne su ka hallaka biyo bayan harin jirgin yaƙin ta sama akan matsugunin ƴan gudun Hijira a jihar River Nile da ke ƙasar Sudan, gwamnan jihar a cikin wani jawabinsa ya bayyana cewa harin ya katse babbar tashar samar da wutar lantarkin yankin gaba ɗaya a karo na hudu.

Ƙungiyar tsaro ta RSF ta musanta kai harin jirgin saman kuma ba ta bayar da wani martani akai ba, sai dai daman tuntuni ta na kai hari kan babbar tashar lantarkin a yankin da ke ƙarƙashin kulawar sojoji a tsakiya da arewacin na Sudan tsawon watanni da su ka gabata.
Wata malama shaidar gani da ido mai suna Mashair Hemeidan ta bayyana cewa, sun ji wata ƙarar fashewar abu da safe inda bayan sun duba su ka ga iyalai guda biyu sun ƙone ƙurmus a matsuguninsu, a yayin da su ke bacci.

Ta kuma ƙara da cewa sun baro birnin Khartoum saboda su na tsoron yaƙi amman yanzu gashi yaƙin ya biyo su har inda su ke, ba ta san yanzu inda za ta je da iyalai da ƴaƴanta ba, ba su da wani muhalli ko wurin zuwa.

Yanzu haka ana ci gaba da fafata ƴakin gumurzu ne a yankin Darfur, inda ƙungiyar tsaro ta RSF ke matsa lamba don ganin ta ƙwace sauran inda sojojin su ke, tare da fitar da dubunnan ɗaruruwan mutane daga gidajensu.
Ko a harin da aka kai da safiyar ranar Juma’ar na makami mai linzami wanda ya ƙone matsugunai da yawa, ya jikkata mutane 23 kamar yadda wani jami’in kula da lafiya ya bayyana.
Inda a ranar aka ga jami’ai da hukumomi su na tattara kayayyakin da wutar ta lalata tare da rufe matsugunin, inda aka ga an kwashi mazauna wurin a manyan motocin safa-safa zuwa wani wurin na daban.