Jagaliya na nufin biyayya ko goya baya ga duk wani shugaba, ko wani ɗan takara mai neman wata kujera, ko kuma wani  mai muƙami irin na siyasa akan duk wani ra’ayi mai kyau ko akasin sa dan samun biyan bukatar kai batare da la’akari da illa ko amfanin wannan lamari ga al’umma ba.
Ɗanjagaliya kuma na nufin duk mai yin siyasar banbaɗanci ga ɗan takara ko wanda ake bashi kayan maye da nufin sha ya bugu ya aikata abinda bai dace ba, dan biyan buƙatar wani ɗan takara ko mai riƙe da muƙamin siyasa.
Illar harkar jagaliyanci

Ɗan jagaliya a ko da yaushe yana yin abin da zai farantawa mai gidanshi rai ne, saboda     biyan buƙatarshi da iyalan sa ba  don cigaban al’umma ba, duk matsayin sa a gwamnati , komai zurfin ilimin sa komai matsayin sa a mataki na siyasa, koda kuwa ya tara  miliyoyin kuɗaɗe.
Ina ɗan jagaliya ya sa gaba ?
Abin tambaya anan shine ɗan jagaliya da ake bashi kayan maye da yawo da makami ko ya sari abokin hamayya wato ɗan wata     jam’iya me ribarsa a rayuwa, ?.
Mafi aka sari da zarar ɗan jagaliya ya aikata wani laifi aka kamashi, to iyayen gidansa ne suke karɓo shi daga hannun ƴan sanda, to amma fa shima sai uban gidan nashi ya sanshi shine zai tsaya masa.
Me makoman ɗan jagaliya a rayuwa ?
Ɗan jagaliya bashi da tsari na cigaba a rayuwa na yadda zai gina rayuwarshi kamar yadda yake ƙoƙari wajen ganin ya gina rayuwar uban gidanshi da iyalansa.
Dalili kuwa shi bai je makaranta ba, sannan bai koyi wata sana’ar dogaro da kai ba, ta wace hanya zai gina rayuwarshi face lalata rayuwarshi ta hanyar shaye shaye, da sare sare,.
A ko da yaushe ana kiraye kiraye kan matasa su kauce wa bangar siyasa, kamar yadda ƙungiyoyi na ciki da waje ke ta kiraye kiraye amma sam saƙon baya zuwa gare su,    kasancewar basa bibiyan kafafen yaɗa labarai don jin saƙonnin da ake isar musu.
A wannan lokaci nima ina isar da wannan saƙo ne ga wanda suke assasa wannan harka ta jagaliyanci da matasa ke faɗawa.
Abin da ya janyo hankali na kan wannan batu shine ganin muna dab da yin zaɓen 2019, ta ƙasa baki ɗaya sai gashi a zagayen da ƴan takara kan yi ƙananan hukumomi , ko Mazaɓu don neman  magoya baya, sai gashi an fito da wani sabon salo na ƙwace a loƙacin da ake gudanar da wannan gangami, wannan abu ya ta’azzara a wannan lokaci wannan ba           ƙaramin barazana bane ga alumma da ma su kansu matasan.
Jami’an tsaro na iya ƙoƙari wajen daƙile     wannan matsala amma abin kamar ba’ayi kasancewar kullum ya kan zo da sabon salo ne.
Wace gudunmawa kafafen Yaɗa labarai zasu bayar wajen wayar da kan matasa da su guji harkar jagaliyanci ?.
Kafafen yaɗa labarai sun daɗe suna wayar da kan matasa kan illar jagaliyanci, ta hanyar shirye shiryensu da suke gabatarwa musamman wanda suka shafi matasa.
Kamar yadda Mujallar matashiya take gabatar da wani shiri na            musamman mai suna Don matasa a sashinta na talabijin dake youtube.
Sai dai inda gizo ke saƙar shi ne ba lallai bane a ce wanda ake shirin don su saƙon yana isa gare su.
Wace hanya za’abi wajen magance wannan matsala ta jagaliyanci ?.
Ni a ganina kamata yayi a sauke yaƙin neman zaɓe kawai na tara al’umma duk ɗan takara ya dinga yawon ziyara gida gida don neman a goya masa baya tare da bayyana manufofinsa, da kuma yin alƙawura na idan ya samu nasara ga aikin ta zai yi ko kuma ƙudiri da zai kai.
Ko kuma a koma bayyana manufofi ta hanyar kafafen yaɗa labarai da na sada zumunta.
Wannan shine ra’ayi na.

Leave a Reply

%d bloggers like this: