
Ci gaba
Ta kuma hada ne da alamu wadanda suka hada da kamar amenorrhoea, hirsutism, wani al’amarine wanda ya shafi rashin haihuwa. Ita wannan matsala tana samar da raguwar samar da sinadarin FSH da kuma yadda aka saba ko kuma ƙaruwar mizanin LH, estrogen da kuma testosterone, shi dai wannan hasashen ko kuma ikirarin wanda yake da dangantaka da shi halin yana samar da ɗan ƙaramin girma ne nan a wasu sinadaran obary follicles da kuma obarian follicles and follicular cysts, wadannan ana iya gano su ta hanyar daukar hoton na dakin gwaji. Shi wannan sinadari na obary zai kasance wasu abubuwa masu santsi sun zagaye shi, wadanda suka yi kama da kafso, wanda zai iya karuwa har sau biyu. Shi mizanin da ya ƙaru na oestrogen yana iya zama sanadiyar kamuwa da cutar kansar Nono. Irin wannan matsalar tana da alaka da rashin sinadarin abinci wanda ya ƙunshi carbohyrate metabolism, musamman ma yadda abin zai samu matsala da Insulin. Insulin wani sinadari ne wanda yake cikin jikinmu wanda yake taimaka mana wajen yadda zai daidaita sikari a jikin mu. Wannan an yi sa’a shine idan anbi dokoki da kuma ka’dojin abinci da kuma yin amfani da magani mai rage kaifin cutar sikari kamar Thmetformin. Su thyroid gland da kuma adrenal suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo matsala ta rashin haihuwa. b) Rashin aiki saboda matsalar hypothalamus Shi hypothalamus wani bangare ne na ƙwaƙwalwa wanda shi aikin shi shine isar da sako zuwa ga pituitary gland wanda kuma daga can sai ya aika zuwa obaries a matsayin wani sinadari na FSH da kuma LH wadanda kuma su zasu taimaka wajen kwai ya kai mizanin da ya kamata. Ana iya daukar al’amarin a matsayin mai taka muhimmiyar rawa wajen shigar ciki, amma idan shi sinadarin hypothalamus ya kasa taka rawar shi sosai a cikin halin ana iya samun matsala ta samun kwai amma fa wanda bai kai lokacin da ya kamata ba. Wannan shi ke samar da matsala ta obarian har kashi 2

