Tare da Malam Dayyib sadi Gaida

Abu ne sananne a wurin dukkanin musulmi dama wadanda ba musulmi ba cewa addinin musulunci ya bada cikakkiyar kulawa a bangaren tarbiyya, idan  kace gabadaya addinin musulunci sunansa tarbiyya bakayi   kuskure ba.

ALLAH subhanahu          wataala ya aiko                annabawa daban daban ga alumma daban daban duk domin tabbatar da ko kuma gyaran tarbiyya, hakan yasa aka saukar da littattafai da dama, kamar su attaura da injila da zabura da kuma alqurani mai girma, kuma aka ware malaika guda      wanda aukinsa kawai saukar da wahayi ga annbawa, duka dai domin tabbatar da ko kuma    gyaran tarbiyya.

Idan muka koma baya, wato asali ko kuma ince tushe,yadda  zamuga          ALLAH          subhanahu        wataala ya     shirya tsarin tarbiyya ga    fiyayyan halitta             annabinmu Muhammad saw, ta yadda aka haifeshi maraya, ba uba kuma              mahaifiyar sa bata wuce    shekara        shida ba ta      koma ga, ALLAH, hakan yasa ya taso hannun dangi cikin kyakkyawar kulawa da tausayawa, malamai sunce anyi haka ne domin a nuna mana yadda ake hada karfi da karfe wajan tarbiyya.

Bayan ya girma ALLAH ya zaba masa mata ta gari, da abokanai na gari, domin samun wadannan jinsi biyu managar ta, wato mace ta gari fa     aboki na gari na     taimakawa wa wajan samun ingattacciyar tarbiyya.
Musulunci ya wajabta tarbiyya, kuma ya fadi wadanda tarbiyya ta wajaba akansu, kuma ya koyar da su yadda zasu tarbiyyantar da wadanda aka daura musu hakkin. Tarbiyyan tarwa.

 

Gyaruwa ko lalacewar tarbiyya tana kan jinsin mutane uku 3 na farko iyaye, na biyu makaranta, na uku muatanan           unguwa., idan wadannan turaku uku sukayi        tsayiwa irinta daka, bisa      kyakyawar niyya kowa ya sauke bakin gwargwadon nauyin da ke kansa na tarbiyya to babu maganar lalacewar tarbiyya awannan          al umma, idan aka samu akasin haka kuwa to sai dai ace inna lillahi wa   inna ialihi rajiun
Nauyin dake kan uwa da uba dangane da tarbiyya.

 

iyaye sune dirka ta farko da hakkin bada tarbiyyar ƴaƴa ta hau kansu, shiyasa manzon Allah saw yace (kowanne abun  haihuwa ana haifarsa ne akan fidrah ta addinin musulunci , sai daga baya iyayansa su maidashi bayahude ko kirister ko kuma bamaguje ) da wannaan zamu fahimci cewa lallai iyaye suke kan gaba da kaso mafi tsoka wajan gina tarbiyya ko rugujewar ta.

 

Mafiya     yawan lokutan yara suna yin sane agida tare da iyaye ,musanman ma uwa mace don haka ya zama wajibi gareta   tayi aiki tukuru wajan sauke nauyin da allah ya dora mata na tarbiyyar    yayanta.kamar yadda   shima uba ya zama tilas ya sauke nasa nauyin,

Nauyin da ke kan makaranta ,    lallai makaranta itace ta dirka ta biyu wajen tabbatar da  ingattacciyar tarbiyya yara

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: