Cutar HIV ta ragu da kashi 2 da ɗigo 8, inda yake kashi 1.4 a ƙarshen shekarar 2018 wanda yayi dai dai da kimanin mutane miliyan 1 da dubu dari 9.
A cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya gabatar da wannan jawabin ne yayin bikin bayyana sakamakon bincike kan illa da kuma yaɗuwar cutar HIV a Najeriya ƙarƙashin kwamitin gudanarwa da aka kafa a shekarar 2018.
Shugaban ya ce rahoton babban cigaba ne A ɓangaren lafiya wanda a shekarar 2014 Najeriya na da yawan masu ɗauke da cutar ta HIV AIDs da suka kai kashi 3.1, wanda kuma aka samu raguwarsa zuwa kashi 1.4 hakan na nuni da cewa ƙasar na kan turbar yaƙar cutar nan da shekarar 2030 kamar yadda ta tsara.
Sai dai shugaban Muhammadu Buhari ya ce har yanzuu lokaci bai yi ba da za a fara murnar yaƙar cutar ba.
Sai wannan rahoton na bana zai ƙarawa ɓangaren lafiya ƙwarin gwiwar cewar ana samun gagarumin nasara a yaƙi da cutar HIV AiDs a Najeriya da sauran cututtuka.