Shararren Ɗan wasan tsakiya Paul Pogba dake Manchester United zai bukaci albashi mafi tsoka daga duk ƙungiyar da ta yi masa tayin komawa ƙungiyar su.
Wakilin Pogba, Mino Raiola ne ya bayyana haka yayin sanar da adadin kuɗaɗen da suka tsaida a matsayin albashin da zai nema daga duk ƙungiyar da tayi ƙoƙarin siyan shi.

A cewar Raiola, Paul Pogba ɗan ƙasar faransa na neman albashin euro miliyan 16 a duk shekara, wanda yayi dai dai da dubu 300 na fam ɗin Ingila a kowane mako.
Sai dai ana ganin wannan abu ne mai wahala a samu ƙungiyar da zata iya viyan wannan maƙudan kuɗaɗen ga ɗan Wasa Pogba.
Wakilinsa Raiola ya jaddada aniyar sa ta ganin Pogba ya zama ɗan wasa mai ɗaukar albashi mafi tsoka a Real Madrid ko Juventus dake zawarcinsa, da ƙungiyoyin suke, muddin yarjejeniyar ta kullu tsakaninsu da kowacce ƙungiya wadda ta amince zata ɗauki dan wasan
To za’a sallama musu shi.

