Kamfanin mujallar matashiya ta buga wasan sada zumunta da kungiyar masu shirin barkwanci (Comedy) reshen kasuwar waya ta farm centre dake jihar kano.

Wasan dai Da aka buga Matashiya tayi nasarar zura ƙwallaye 10, inda ƴan comedy suka zura kwalllaye 3.
An dai buga wasan ne a ƙaramin filin wasan Ƙwallon ƙafa ta La Sultana.

Cikin wanda suka zura wa Matashiya ƙwallaye akwai Aminu wanda ya zura ƙwallaye 4, a yayin da Ibrahim Bala ya zura kwallo 2, da sauran ƴan wasa da suka zura ragowar ƙwallaye.

Wannan ne dai karo na farko da kamfanin mujallar Matashiya ta buga wasan sada zumunta inda ta fara da Nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: