Da yawan mutane na fama da tsananin sha awa sai dai wasu na rasa yadda za su saka kansu.

A wasu lokutan wasu kan yi amfani da hannunsu wajen biyawa kansu buƙata, kamar yadda wata ta aiko da tambaya ta cikin shirin da muke amsa tambayoyin da kuke aiko mana a bisa tafiyar rayuwar addinin musulunci.
Wata baiwar Allah ta aiko da tambayar cewa za ta iya biyawa kanta buƙata da hannunta saboda tsananin sha awa?

Shek Muhammad Tukur Moriki ne ke amsa tambayar ya kuma ce, biyawa kai buƙata da hannu tamkar mutum ya aikata zina ne.

Kuma duk mutumin da ya kasance mai auren hannunsa Allah S.W.A ya tsine masa, sai in har ya tuba daga aikata hakan.
Malam Moriki ya ce akwai hanyoyi da mutum zai iya katange kansa, misalin yin azumi, da kuma kaucewa kallon abinnda zai tada hankali izuwa sha awa.