Ƙungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta gabatarwa da kungiyar Tottenham tayin mika mata tsohon ɗan wasanta Gareth Bale a matsayin aro kan euro miliyan 10.
A shekarar 2013, ne dai Bale ya koma Real Madrid daga Tottenham kan euro miliyan 86, abinda ya sa shi zama ɗan wasa mafi tsada a waccan lokacin.
Tun a wancan lokacin Bale shine yafi kowa samun albashi mai tsoka tsakanin ƴan wasan ta Real Madrid, inda yake karɓar fam dubu 600 adukkanin mako.
A baya bayan nan,dai ɗan wasan na fuskantar ƙalubalen nuna na rashin nuna kwazo a wasannin da yake bugawa, lamarin da yasa yake fuskantar suka daga mafi akasarin magoya bayan Real Madrid.
Hakan yasa tilas ƙungiyar ta yanke shawarar siyar dashi ka masu buƙatarsa, sai dai har yanzu babu ƙungiyar da suka nuna sha’awarsu ga ɗan wasan, hakan yasa Ƙungiyar Realmadrid ta yanke shawarar ba da shi a matsayin Aro ga tsohuwar Ƙungiyarsa ta Tottenham dake ƙasar Ingila.


