Mai martaba sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar Ila Autan Bawo ya bayyana cewar akwai ƙasar Rano wadda ke cikin Hausa bakwai tun shekaru 300 kafin zuwan Annabi Isa.

Sarkin Rano ya bayyanawa mujallar Matashiya cewar dawo da darajar masarautar abin alfahari ne tare da ɗaukar azamar cigaba da ayyuka tuƙuru na yadda al’umma za su amfana.

 

Cikin zantawa da ya yi da mujallar Matashiya ya ce ƙasar Rano na da daɗaɗɗen tarihi wanda duniya ma ba za ta manta da shi ba ganin manyan al’adu da ke kewaye da garin.

Batun nasarorin da ya samar a matsayinsa na sarki kuwa, mai martaba sarkin rano ya bayyana ɗumbin nasarorin da ya samawa al’ummarsa tun bayan hayewa kan karagar mulki, nasarorin da suka haɗa da inganta ilimi, harkokin kasuwanci da kuma ɓangaren lafiya.

 

Haka kuma ya bayyana cewar masarautar Rano dama tun fil’azal tana da daraja ta ɗaya a halin yanzu dawo da wannan darajar aka yi don haka ba sabon abu bane kamar yadda wasu mutanen ke kuskuren fahimta.

Sannan ya ja hankalin hakiman da ke ƙarƙashinsa da su kasance masu ƙoƙarin kawo hanyoyin da al’ummar masarautar za su cigaba kamar yadda ya yaba da ƙoƙarin da suke yi a baya.

Za ku iya kallon hirar a dandalin mujallar Matashiya da ke youtube.

Leave a Reply

%d bloggers like this: