Wata matashiya ta Haihu ana tsaka da Rubuta jarabawa a kwalejin Yankin mamou dake kasar Guinea Conakry, daga bisani ta dawo ta cigaba da Rubuta jarabawar.

matashiyar mai suna Fatoumata Kouramou yar shekaru 18 ta bayyana cewa dalilin da yasa ta dawo wa Rubuta jarabawar Phisics Bata son maimaita aji ne Wanda ta shafe shekaru tana so ta kawo karshen karatun nata na diploma shi yasata dawowa ta cigaba da Rubuta jarabawar bayan ta Haihu da minti goma zuwa Arba’in.

Mijin fatimatou Dan sanda ne mai mukamin Copral ne da yaji labarin irin jarumtar da matarsa tayi ya yaba mata matuka tare da fatan Allah ya Raya musu Yaron da suka Haifa.

Suma Alummar Yankin mamou town da malaman jamiar sun yaba wa fatimatou irin jarumtar da ta nuna da kuma kishin Ilimin da take dashi hakan ne yasa ta sadaukar da rayuwarta don ganin ta samu shaidar Diplomar ta ba tare da matsala ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: