Daga Sadisu Muhammad

Kungiyar kwallon Kafa ta Jigawa Golden Star FC Ta Samu Nasarar Shiga Gasar Premier league ta kasa Nigeria.
A jiya litinin kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden star ta samu Nasarar samun Tikita buga Gasar Premier league ta Nigeria bayan da ta samu Nasarar Lallasa kungiyar kwallon kafa ta NAF FC Abuja da ci 3-2, a garin Jos dake jihar plateau.

Kugiyar ta Jigawa ta samun wannan Dama ne tun bayan shekaru 9 da suka Fado daga Gasar, kungiyar ta samu wannan Nasara ne karkashin Jagorancin mai horas da kungiyar Rabiu Tata wanda tsohon dan wasan Kungiyar kwallon kafar Jigawa ne, kuma Mazaunin Gwagwarwa a karamar hukumar Nasarawa dake jihar kano,
Wakilin Mujallar Matashiya Sadisu Muhammad ya tattauna da Mai Horas da kungiyar Jim kadan bayan kammala wasan inda Rabiu Tata ya godewa Allah, da wannan Nasara daya samu ganin cewa wannan Tarihi ne babba daya kafa akan harkar kwallon kafar Najeriya,
Daga karshe Mai horas da kungiyar ya godewa yan wasa da magoya shugabanni da kuma Gwamna Badaru Abubakar bisa Kulawa da suka samu tare da basu cikakken gudunmawa.
Zuwa yanzu kungiyon kwallon kafa hudu da suka hauro gasar premier ta kasa sun hada da=

Jigawa golden Stars
Adamawa United
Akwa starlets
Warri wolves
.