Kasashe dake da hannu kan
yarjejeniyar nukiliyar Iran sun gudanar da wani taron a kasar Australiya da nufin kawo karshen matsalar yarjejeniyar tun bayan da Amurka ta sanar da yi watsi da matakin.
Tun bayan kasar Iran tayi zargin rashin mutunta alkawuran da ta dauka a baya.
A Farkon watan Janairu ne dai Iran ta yi watsi da kiraye-kirayen da manyan kasashen duniya suka yi mata na yin biyayya ga yarjejeniyar da aka kulla da ita a shekarar ta 2015 na takaita adadin makamashin Uranium da take yi.
Sai dai kasar Iran ta kafe ne da matsayinta na ranar 8 ga watan 5 cewa, zata yi watsi da yarjejeniyar da aka kulla da ita saboda yadda shugaban Amurka Donald Trump ya kara kakaba mata takunkumi.
Shugaban Iran Hassan Rouhani yace matakin su ya biyo bayan rashin cika alkawari ne da aka nuna masu, gashi kuma an gaza yin komi dangane da takunkumin da Amurkan ta kakaba mata.kamar yadda Rfi ta rawaito.

Leave a Reply

%d bloggers like this: