Da Alamu Tattaunawa dake tsakanin yan Kungiyar Taliban Da kasar Amurka kwalliya zata biya kudin sabulu, inda ake ganin za’a kawo karshen yaki mafi muni da ya daidaita Al’ummar kasar Afghanistan.

Majiya mai karfi daga fadan Shugaban kasar Amurka na bayyana cewa muddin yan Taliban suka mutunta Yarjejeniyar dake tsakaninsu tabbas Zata mara mata baya.
Suna a nasu jawabin Kungiyar Taliban sun bayyanawa manema labarai cewa suna da karfin gwiwa a baya amma dai har yanzu akwai sauran Rina a kaba a cimma Yarjejeniyar.

Haka zalika Taliban ta bukaci Shugaban kasar Amurka Donald Trump da ya janye sojojinsa daga yankinsu kafin zaben shekara mai zuwa.
