Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi suka tare da nuna bacin ransa kan masu kyamar Bakake tare nuna wariyar Launin fata.

Shugaban yayi Kira akan zartar da hukuncin kisa akan duk Wanda aka samu da laifin kisan gilla.
Trump yayi wanna jawabi ne a fadar White house biyo bayan kisan gilla da Wasu mahara sukayi a jihar Texas da Ohio inda suka hallaka mutane mutane 50.

Tuni Shugaba Trump ya bada umarnin hukumar Bincike ta FBI da su binciko maharan tare da daukar mataki mai tsauri don dakile laifukan kyamar Bakake da Ta’addanci a kasar Amurka.
