Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Mu shaƙata

Yadda Rahma Sadau ta haifar da zazzafar muhawara a Twitter

Yadda Rahma Sadau ta haifar da zazzafar muhawara a Twitter

Shafukan sada zumunta a Najeriya sun zama wani wuri guda daya tilo dake hada al’umma wuri guda, inda zaka iya ganin halin da sauran al’umma ke ciki daga sassa daban-daban, baya ga wannan al’umma kan bayyana ra’ayoyinsu ko wallafa duk abinda suke so tare da tafka muhawarori akan batutuwa daban-daban da suke da bukatar tsokaci akai.

 

A wannan makon an samu wata zazzafar muhawara da aka dau tsawon lokaci ana tafkawa wadda kuma har izuwa wannan lokaci ba’a kai ga karkareta ba, muhawarar ta samo asali ne bayan da daya daga manyan jaruman fina-finan Hausa, Rahma Sadau ta wallafa wasu zafafa kuma fitattun hotuna a shafinta na Twitter, wanda kan mabiya shafin ya rabu gida biyu wasu na ganin jarumar tayi dai-dai a gefe guda kuma wasu na ganin jarumar ta wuce kima wajen sanya hotunan domin a cewarsu hotunan sun sabawa al’adar malam Bahaushe.

Ana tsaka da tafka wannan muhawara ce kuma kwatsam sai wani mai amfani da shafin na Twitter mai lakabin Error ya canja salon muhawarar bayan da ya fito ya bayyana ra’ayinsa wanda ya roki jaruma Sadau kan ta daure tayi musu film din badala ko guda daya ne.

Wannan batu sai ya kara zafafa muhawarar inda mutane da dama suka rika bayyana ra’ayinsu akai, kan kace kwabo labarin ya baza duniyar hausawa a Intanet, ‘yan Instagram sun dauka, ‘yan YouTube suma sun dauka, masana na kallon wannan wata damace da Error yayi amfani da ita ya tallata kansa.

Dama dai ba wannan ne karon farko da jarumar dama wasu sauran jaruman Hausa ke wallafa zafafan hotuna da kan jawo cece kuce a shafukan soshiyal midiya ba.

 

Allah ya kyauta.

 

Sharhi: Basheer Sharfadi  

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: