malaman musulunci na duniya sun kadu kan ihu da cin zarafin da wasu yan kwankwasiyya su ka yi wa fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Nigeriya, DR. Isah Ali Ibrahim Pantami, inda Wasu gungun manyan malamai a ƙasar Saudiyya suka yi Allah wadarai da wannan al’amari tare da bayyana lamarin a matsayin ɗabi’ar rashin ɗa’a da rashin ganin girman Littafin Allah qur’ani da kuma tozarta mahaddatansa.

A dan haka ne ma malaman su ka yi kiran gaggawa ga shugaban ƙasar Nigeriya Muhammadu Buhari da gwamnan Jihar Kano, DR. Ganduje su ɗauki matakin gaggawa wajen zaƙulo matasan da su ka aikata wannan ɗanyen aiki tare da hukunta su don ya zama izina.

A cewar malaman, Malam Isah Ali Pantami ya na zaman-zamansa a birnin Madina gwamnatin Nageriya ta bukaci da ya zo ya ba da gudunmawarsa wajen ciyar da ƙasarsa gaba, kenan da hakan ya zama a wajibi a kare masa daraja da mutuncinsa, domin hakan ne zai kara masa karfin gwiwa da kuma ba wa wasu malaman ma damar yi wa kasarsu hidima a duk lokacin da aka bukace su ko da nan gaba.

Madogara
Muryar yanci/ matashiya

Hoto/ liberty/Muryar yanci

Leave a Reply

%d bloggers like this: