Ministan Albarkatun man kasar Saudiya Yarima Muhammad Salman yayi gargadin cewa farshin danyan mai ka iya tashin gwauron zabi a kasuwar Duniya, muddin aka kasa daukar mataki akan kasar Iran.
Yarima ya kara da cewa akwai yuwuwar matsalar Tattalin Arziki Arzikin Duniya ka iya Tabarbarewa sakamakon Rikicin dake faruwa tsakanin Saudiya da kasar Iran.
Tun bayan harin da aka kai matatar man kasar Saudiya makonnin baya ake takun saka tsakanin kasashen biyu.
Inda ake.zargin kasar Iran da kitsa harin, inda ake zaton harin ka iya zama barazana ga Tattalin Arzikin kasar da na Duniya baki Daya.