Rahotanni daga Hukumomin kasar Saudiyya, sun tabbatar da bullar cutar Corona Virus a kasar.
wannan cutar Coronavirus, wacce ake yiwa lakabi da COVID-19 ta bulla ne a ranar litinin a kasar, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana.
A cewar Hukumar Wanda ke dauke da cutar dan asalin kasar Saudiyya ne, ya taho daga kasar Iran ne, inda ya yada da zango a kasar Bahrain.
ma’aikatar lafiyar kasar ta ce yanzu haka mutumin na nan a killace a asibiti, sannan tuni an fara aikin gwada duk mutanen da ya yi mu’amala da su tunda ya shigo kasar don ganin an dakile yaduwar cutar a kasar.


