Ministar kudi Hajiya Zainab Ahmed shamsuna ta bayyana cewar ” gwamnatin tarayya ta dakatar da aniyar ta na ranto dalar amurka biliyan 27,
A cewarta any dakatar da shirin ciwo bashin ne saboda matsanancin halin da tattalin arzikin duniya ke ciki a halin yanzu.

Ministan ta bayyana hakan ne a jiya litinin a babban dakin taro na kasa dake babban birnin tarayya Abuja.
A taro na musamman da aka shirya wanda ya shafi hada-hadar cinikayya da ma’ikatar SEC ta shirya.

Ministar tace ” duk da yake gwamnatin tarayya ta mika bukatar ciyo wannnan bashi gaban majalisa dattawa, amma koda ‘yan majalisar sun amince, ba za’a karbo bashin ba.

Karyewar farashin albarkatun mai a kasuwannin duniya sakamakon annobar cutar Corona virus sun tsayar da tattalin arzikin duniya wuri daya,
shine dalilin da yasa aka ga ya dace a mai da hankali akan sauran abubuwan da suke kawo wa kasar kudi da kuma neman sabbin dubarun bunkasa tattalin arzikin Kasar Najeriya.

Gwamnatin tarayya zata maida hankali kan muhimman ayyuka kafin daga baya idan tattalin arzikin ya dawo hayyacinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: