Cutar coronavirus ta kama Firai Ministan Birtaniya, Boris Johson, kuma tuni ya killace kansa.

Cikin wata sanarwar da ya fitar da kansa, Boris Johnshon yace “bayan ya ji alamun rashin lafiya a sa’a 24, an yi mishi gwaji kuma sakamakon ya nuna ya kamu da coronvirus.”
Ya kara da cewa ”Yanzu haka ya killace kanshi, amma za cigaba da jagorantar yaki da Cutar a fadin duniya

Ita ma Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar ta bayyana cewa Boris Johson zai ci gaba da jagorantar gwamnatin Birtaniya a yaki da cutar a fadin duniya.
