Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa, za a samar da alluran riga-kafi annobar COVID -19 kafin karshen wannan shekarar, wanda tace zai iya kaiwa biliyan 2 a shekarar 2021.

Yayinda aka fantsama wajen samar da maganin rigakafin na Corona,
Daraktar Kimiyya na WHO Soumya Swami-nathan ta ce, yanzu haka akwai kimanin magungunan daban-daban har 200 a fadin duniya da ake gwaje-gwajensu a asibitoci,

wanda tace, za’a iya dacewa da daya ko biyu kafin karshen wannan shekara.

Babbar jami’ar hukumar ta WHO ta bayyana rukunin mutane uku cikin al’umma da tace, za’a fara baiwa maganin da zaran an same shi, da suka hada da jami’an kiwon lafiya da na ‘yan sanda da kuma gajiyayyu.