Daga Maryam Muhammmad

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi
Umar Ganduje ya kaddamar da wani kwamiti dazai tattara bayanai akan shugabancin dattawa na jam’iyyar APC.

Kwamitocin wadanda aka rabasu izuwa mazabun sanatoci uku na jihar kano, anasaran su tattara bayanai akan matsalolin da jam’iyyar APC ke dasu a kananan hukumomi da mazabu da nufin lalubo bakin zaren.

Kwamitocin dai zasu karbi bayanai ne daga kananan hukumomi, a kano ta kudu an nada Kwamishinan raya karkara Hon Musa Iliyasu Kwankwaso amatsayin shugaba , sai kano ta Arewa Dakeda Kwamishinan kasafi da tsare tsare Nura Muhammad Dankadai, sai kuma Kano ta tsakiya karkashin jagorancin Kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo.

Gwamna Ganduje ya kafa wani kwamitin na mazabu kazalika da Babban kwamitin da zai karbi rahoton kwamitocin karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Kano Alh Usman Alhaji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: