Akalla mutane shida wanda akasarinsu yara ne sun mutu a yayin da wani bam ya tashi a Arewacin kasar Burkina Faso.
Shaidun gani da ido sun ruwaito cewa, bam din ya tashi ne a yayin da al’umma ke dawo daga hada-hadar yau da kullum a lokacin bukukuwan Sallah, wanda ya janyo jikkatar wasu mutum hudu.
Arewacin kasar Burkina Faso ya shahara a matsayin yankin da ‘yan ta’adda ke kai hare-hare wanda tun daga shekarar 2015 kawo yanzu, fiye da rayuka 1,000 sun salwanta yayin da kuma akalla mutum miliyan daya sun tarwatse daga matsugunansu.
Mutanen da fashewar bam din ya ritsa da su galibi kananan yara ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga kiwo kamar yadda wani jami’i birnin Ouahigouya ya bayyana.
Hare haren bama-baman na cigaba da karuwa ne tun daga shekarar 2018, inda akalla rayukan dakarun soji da na farar hula 200 sun salwanta kamar yadda alkaluman kamfanin dillancin labarai na AFP suka nuna.