Connect with us

Siyasa

Adam Zango zai yiwa Atiku waƙar kiranye idan kowa ya tura 500

Published

on

Mawaƙin ya wallafa hakan ne a shafinsa na Instagram cewa yanaa so ya yi zazzafar waƙa don yowa Atiku kiranye.

Fitaccen mawaƙi kuma jarumi a masana antar fina finan Hausa Adam Zango ne ya bayyana hakan cikin wani faifan bidiyo da yayi.

Ya ce tunda aka yi zaɓe tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya tafi dubai, kuma yana son yin waƙar ne don yi masa kiranye.

Ya cigaba da cewa a wannan lokaci ba su samu abinda suke buƙata ba a dangane da zaɓen da aka yi a shekarar 2019, don haka ya nemi masoyan Atiku ƴan Najeriya da kowanne mutum guda ya tura naira 500 don yiwa Atiku waƙa.

Hakan na zuwa ne kwana ɗaya rak da tattaunawarmu da mawaƙi Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara da ya nemi masoya Buhari su tura naira 1000 kowanne don yiwa shugaban kasar waƙa tare da nuna ayyukan da ya yiwa kasa.

1 Comment

1 Comment

  1. yusifhassan18@gmail.com

    September 12, 2020 at 11:30 am

    where is the account number please

Leave a Reply

Siyasa

APC Ta Yi Watsi Da Zaɓen Shugabannin Ƙananan Hukumomi A Jihar Osun

Published

on

Jam’iyyar APC ta yi Allah wadai tare da yin watsi da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata a jihar Osun, ƙarƙashin jagorancin gwamna Ademola Adeleke na jihar da jam’iyyarsa ta PDP.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa Felix Morka ne ya bayyana hakan jiya Lahadi a birnin tarayya Abuja, inda ya bayyana zaɓen a matsayin haramtacce da kuma bijirewa umarnin kotu.

Ya bayyana cewa kotun ɗaukaka ƙara ranar 10 ga watan Fabarairu ta tabbatar da dawo da tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin jihar da Adeleke ya sauke, hukuncin da ya warware umarnin babbar kotun tarayya na ranar 22 ga watan Nuwamban shekarar 2022.

Morka ya ƙara da cewa hukuncin kotun ɗaukaka ƙara tuni ya warware umarnin kotun baya, tare da tabbatar da shugabannin ƙananan hukumomin akan kujerunsu har zuwa ƙarshen zangon mulkinsu a watan Oktoban shekarar nan ta 2025.

Ya kuma soki tsarin na gwamna Adeleke wanda ya naɗa kantomomin riƙo da cewa ya saɓa da sashi na 7(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya, tare da bayyana cewa jam’iyyarsu ta APC tana girmama hukuncin kotu.

A ƙarshe Felix ya yi kira da jami’an tsaro da su sanya ido dan tabbatar da zaman lafiya, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa halastattun shugabannin ƙananan hukumomi da kotu ta yarda da su ne za a bai’wa kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Continue Reading

Siyasa

Za Mu Karɓi Jiga-Jigan Ƴan Jam’iyyar NNPP Zuwa Jam’iyyar APC A Kano – Ganduje

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, jam’iyyarsu ta APC ta shirya karɓar wasu jiga-jigan ƴan siyasa daga jam’iyya mai mulkin jihar Kano ta NNPP.

Ganduje ya bayyana hakan ne jiya Lahadi yayin rabon motoci da babura ga shugabannin jam’iyyar APC na ƙananan hukumomi da mazaɓu a jihar Kano, wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma sanatan Kano ta Arewa Barau I. Jibrin ya ɗauki nauyi.

Ganduje ya ƙara da cewa rabon kayan ba wai ina na ƴan jam’iyyar APC ba ne, har da dukkan sauran al’ummar jihar, saboda zai bunƙasa rayuwar al’ummar da samar da damarmakin ayyukan yi a tsakankaninsu.

Kowanne shugaban jam’iyya a ƙaramar hukuma ya rabauta da samun mota, yayin da shugabannin jam’iyya a mazaɓu 484 na jihar su ka samu kyautar babura, inda a take a wajen taron kowa ya karɓi takardu da kuma ɗaukar kasonsa.

Yayin da ya ke jawabi a wajen taron Ganduje ya bayyana cewa, dubunnan ƴan jam’iyyar NNPP ne su ke daf da shigowa jam’iyyar ta su ta APC nan ba da daɗewa ba, ciki kuma har da manya-manya ma su riƙe da muƙamai, inda ya bayyana jam’iyyar ta NNPP a matsayin matacciya marar rai.

A nasa jawabin Sanata Barau I. Jibrin ya bayyana cewa, shirin somin taɓi ne kawai na babban rabon kayayyakin da za su yi da aka fara da shugabannin jam’iyya, wanda zai taimakawa al’umma daga rukunai daba-daban.

Continue Reading

Siyasa

Yanzu Malamai Sun Koma Gogayya Da Ƴan Siyasa Wajen Neman Iko – Sule Lamido

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya bayyana damuwarsa game da yawan kutsen malamai cikin harkokin siyasa, inda ya ce yanzu malamai su na matuƙar kwaɗayin samun iko akan masu zaɓe da kuma harkokin gudanar da siyasa.

Lamido ya yi wannan kalami ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, yayin ziyarar ta’aziyya ga Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a Kaduna, biyo bayan rashin babban ɗan sa da ya yi.

Tsohon ministan harkokin wajen na Najeriya ya bayyana cewa yanzu malamai sun samu ikon sarrafa dandalin siyasa, inda su ke yin yaƙin neman zaɓe wani ɗan takara a buɗe kuma su umarci magoya bayansu da da wanda za su zaɓa.

Lamido ya ce duk da baiwar da Allah ya yi musu na zamtowa jagororin addini yanzu su na ƙoƙari ne don samun iko, sai dai kuma malaman kamata ya yi su zamo masu ɗora ƴan siyasar a hanyar da ta dace amman tunda su na son iko, to su ƴan siyasar za su koma gefe su basu fagen.

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa kamar yadda jam’iyyun siyasa su ke fama da rikicin cikin gida to su ma haka malaman addinin su ke fama da rarrabuwar kawuna, tare da gargaɗin cewa dandalin siyasar Najeriya zai ci gaba da zama cikin rikici har sai an samar da haɗin kai.

Idan za a iya tunawa dai a shekarun baya, an ga yadda shugabannin addinai su ka dinga wayar da kan mutane akan karɓar katin yin zaɓe, da kuma yayin zaɓen shekarar 2023 yadda aka samu rabuwar kai a masallatai da coci-coci wajen tallan yan takara.

A kwanan nan kuma an ga yadda batun taron makaranta Al-Qur’ani da aka shirya yi ya yamutsa hazo, inda aka yi niyyar tara mutane 30,000 ma rubuta, makaranta da mahaddatan Qur’ani.

Continue Reading

Trending

%d bloggers like this: