Babbar jam’iyyar APC a Najeriya ta dakatar da babban taron da ta shirya gudanarwa a ranar 26 ga watan da mu ke ciki.

Dakatar da taron ya zo ne kwatsam bayan da uwar jam’iyyar ta ƙasa ta fahimci akwai rikice-rikice a cikin jam’iyyar a matakin jihohi da kuma shyya.
A wata wasika da shugaban jam’iyyar na riƙo Maimala Buni ya sanyawa hannu a yau Litinin sun ce aun aikewa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC domin sanar da ita halin da ake ciki.

Jam’iyyar ta nuna rashin daɗin faruwar hakan amma ta ce wannan ce hanya mafi sauki da za ta kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke faruwa a cikin jam’iyyar.

Ko a jihar Kano ma jam’iyyar APC na fuskantqr kalubale a jihar Kano duk da cewar wata babbar kotu a Abuja ta tabbatar da shugabancin jam’iyya ɓangaren gwamnan jihar a matsayin halastacce.
A nasu ɓangaren, tsagen shugabancin jam’iyyar wanda sanatan Kano ta stakiya Malam Ibrahim Shekarau ke jagoranta sun ce za su ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da kotun ta yanke domin ba su gamsu da shi ba.