Hukumar lafiya matakin farko a Najeriya ta ce ƙasa da mutane miliyan goma kadai aka yi wa riga-kafin cutar Korona a fadin ƙasar baki ɗaya.

Shugaban hukumar Dr. Faisal Shu’aib ne ya bayyana haka ya ce a ranar 25 ga watan Fabrairun da mu ke ciki alƙaluma sun nuna cewar mutane miliyan 8,145,416 ne su ka karbi riga-kafin cutar.
Wannan na nuni da cewar ba a ɗauki hanyar cimma kson da hukumar lafiya ta duniya ke son kai wa na yi wa adadi sama da 80 cikin ɗari riga-kafin ba.

Dr. Faisal Shu’aib ya ƙara da cewa a ranar 25 ga watan Fabrarun, akwai mutane miliyan 17,646,781 da aka yi wa riga-kafin farko ba a yi musu maimai ba.

Haka zalika a ƙasar, an tabbatar da cewar mutane 254,428 su kamu da cutar yayin da aka gwada mutane 4,317,621 da ake zargi.
Daga cikin mutane sama da miliyan 200 da aka samu su na ɗauke da cutar tuni aka sallami fiye da kashi 70 cikin 100 daga cikinsu bayan an ba su kulawa sannan aka tabbatar sun warke daga cutar.
Faisal Shu’aib ya ce akwai buƙatar sake sabon salo don ganin an cimma kaso na adadin mutanen da ake so a yi wa riga-kafin cutar bisa umarnin hukumar lafiya ta duniya domin kawo ƙarshen cutar a fadin duniya.