Ahmad Sulaiman Abdullahi

Rundunar ƴan sandan jihar kwara a ranar Lahadi ta kama wasu mutum biyu da ake zargin matsafa ne ɗauke da sabbon kai da hannun dan adam a tare da su.
Jami’in watsa labarai na hukumar ƴan sanda jihar, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da kamen tare da cewa waɗanda ake zargin suna kan Babur suna tafiya ne a lokacin da jami’an rundunar ‘Harmony’ suka cafke su.

Yana bayyana cewa wadanda aka kaman an gano suna ɗauke da sassan jikin ɗan adam ɗin ne a lokacin da aka tsaresu domin bincike.

Wadanda aka kaman masu suna, Wasiu Omonose, mai shekara 35, da kuma Akanbi Ibrahim, 32, mazauna garin Share da ke karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara
sun kuma faɗa tarkon jami’an tsaron ne a kan hanyar Oke Oyi-Jebba da ke tsakanin karamar hukumar Ilorin ta gabas da Moro, wajajen karfe 11:30 na safe.
Ajayi, ya ce
“Za mu gurfanar da waɗanda aka kaman a gaban Shari’a da zarar muka kammala bincike kan lamarin.
Muna gargadin dukkanin masu aikata laifukan ta’addanci da su gaggauta dainawa domin kuwa hukumar mu a shirye take wajen magance kowace irin kalubalen tsaro.”