Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun kama wani soja da ya ke siyarwa da ƴan bindiga makamai a Abuja.

An kama sojan ne a makon da ya gabata a yankin Dankogi Park a zuba tare da taimakon jami’an tsaron sa kai na yankin.

Sojan da aka kama ya kai wa ƴan bindiga bindiga a kan kuɗi naira 300,000 sannan su ka sake yin jinga domin sake kai wa ƴan bindigan makami a kan kuɗi naira 200,000.

Wani daga cikin ƴan sa kai ya shaida cewar, sojan ya shirya sake kai wa ƴan bindigan wata bindiga ƙirarar AK47 da harsashi a kan kuɗi naira miliyan uku.

Tun da farko ƴan sa kai sun fara bai wa jami’an DSS bayanai a kan zargin da su ke yi a kan sojan kuma daba bisani su ka bayar da haɗin kai aka kamashi.

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa nan da watan Disamban shekarar da mu ke ciki za a kawo ƙarshen matsalar tsrao da ta addabi ƙasar baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: