Rundunar sojin Najeriya ta kuɓutar da wata mata da ƴaƴanta guda huɗu daga hannun ƴan bindiga a Kaduna.

Jami’an tsaron sun ceto matar ne a da wasu mutane uku a yayin da su ke sintiri a babbar hanyar Birnin Gwari zuwa ƙaramar hukumar Chikun a jihar.
Rahotanni sun ce bayan sojoji sun far-wa ƴan bindigan sun gudu zuwa cikin daji.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Kanduna Samuel Aruwan ya sake tabbatar da hakan a yau Talata.

Ya ce mutanen da aka ceto sun miƙa su ga ƴan uwansu a jihar.
Sannan gwamnatin jihar ta jinjinawa jami’an sojin tare da fatan samun wata nasarar a gaba.
Gwamnatin tarayya ta sha alwashin kakkaɓe dukkan ayyukan ta’addanci a Najeriya zuwa watan Disamban shekarar da mu ke ciki.