Masu jiragen sama na kashin kansu a Najeriya sun zi  karar  gwamnatin tarayya a gaban kotu, inda su ke bukatar kotu ta hana  dakatar da jiragen nasu tashi saboda kin biyan kudin fito.

A watan Nuwamban bara ne hukumar hana fasa kwauri ta dakatar da jirage 91 mallakar wasu hamshakan masu kudi, bisa zargin kin biyan kudaden fito da yawansu ya haura naira biliyan 30.

Hukumar Kwastam ta samu sahalewa daga ofishin shugaban kasa, na umartar masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama na hana jiragen daidaiku da ake bi bashin kudin fito aiki.

Sai dai jaridar Punch ta rawaito cewa mamallakan jiragen na neman kotu ta sake duba halascin tursasa musu biyan kudin fiton, kamar yadda hukumar kwastam ke ikrari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: