Biyo bayan kulla yarjejeniya da kungiyar Al-Nassr dake kasar Saudi Arabia a daren jiya Juma’a, Dan wasa Cristiano Ronaldo ya zama mafi yawan daukar Albashi a tarihin kwallon kafa.

A yarjejeniyar da ya sanyawa hannu, Dan wasan zai dinga karbar Yuro Miliyan 200 a matsayin albashin kowacce shekara. Wato kimanin Yuro Miliyan 4 dukkam karshen Mako.

A bayanin kungiyar ta Al-Nassr bayan sun kammala daukar Dan wasan sun ce, wannan babban Nasara ce ka kungiyar tasu Dan ta kara bunkasa.

Kuma sun bayyana cewa, hanya ce da zata kara zaburar da gasar kasar, yara masu tasowa su fahimci kansu. Kuma babban tarihi ne suka kafa.

A nasa bangaren Cristiano ya bayyana cewa, yana farin cikin fuskantar sabon yanayi da kalubale a rayuwarsa a wata kasa da kuma gasa ta daban. Kuma abinda Al-Nassr sukayi Abu ne mai girma.

Ya kuma cewa, zai yi farin cikin haduwa da abokan wasansa a kungiyar. Dan ya taimakawa kungiyar cigaba da samun manyan nasarori.

Zakaran Dan wasan har karo Biyar Na Duniya, yayi matukar son ganin yaci gaba da fafata wasansa a Nahiyar turai. Kuma a babban mataki.

Idan za’a iya tunowa dai Dan wasan sun raba gari da kungiyarsa ta Manchester United ana gaf da tafiya hutun buga gasar cin kofin Duniya. Biyo bayan dangantaka da tayi tsami tsakaninsa da mai horarwar kungiyar Erik Ten Hag.

Leave a Reply

%d bloggers like this: