Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce jam’ian ta ba za su halarci rumfunan zaɓe a ƙurararren lokaci ba.

Hukumar ta ce kayan zaɓe ma ba za a yi jinkirin kai su rumfunan zaɓen ba.

Daraktan wayar da kai a kan zabe Victor Aluko ne ya tabbatar da haka a wajen taron ƙarawa juna sani dangane da babban zabe mai gabatowa.

A gudanar da taro a ɗaƙin taron ƴan jarida na ƙasa da ke Abuja ranar Laraba.
Victor Aluko ya ce hukumar ta riga ta magance matsalar kai kayan zaɓe ko zuwan ma aikatan zaɓe a ƙurarren lokaci.
Sannna ya tabbatar da cewar zaɓen da za a yi nan da kwana tara za su tabbatar ya sha baamban da sauran na baya.
Sannnan ya ce hukumarsu ta ziyarsu masu ruwa da tsaki na ɓangaren man fetur, domin ganin wahalar man ba ta shafi babban zaɓen ba.
Sannan ya shawarci masu yin zaɓe da su ziyarci shafin hukumar na yanar gizo domin sanun rumfunan zaɓensu.
