Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Lahadi ya bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu a girgizar kasar da ta faru a kudu maso gabashin Turkiyya sun kai mutane dubu arba’in da takwas.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kasar wato Erdogan ya kuma bayyana cewa, kimanin mutane dubu d’ari da goma sha biyar ne suka samu raunika.
A jawabinsa ga ‘yan kasa a gidan talabijin a yankin Samandag na lardin Hatay Erdogan yace “yawan mace-macen da aka samu ya kai mutum dubu 48, wadanda suka jikkata kuma sun wuce mutum dubu 115.”

Idan za’a iya tunawa dai ranar 6 ga watan Fabrairun da ya gabata, girgizar kasa guda biyu mai karfin 7.7 da kuma 7.6 ta afku a yankin gabashin Turkiyya bisa tazarar awanni 9 kacal kawai.

Dubannin jijjigar kasar ya shafi yankuna 11 na lardin Turkiyya, da kuma makwaftan kasashe kamar Siriya wacce abin ya fi shafa.