Gwamnatin jihar Kano ta yi kira ga Abba Kabir Yusuf da INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zabe, da ya yi hakuri ya daina fitar da sanarwa ta umarni a matsayin wai shawara, don kada ya kawo yamutsi a jihar.

Wannan ta fito ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammad Garba ya fitar, a yau Juma’a.

Hakan mayar da martani ne ga sanarwar da zababben gwamnan ya fitar jiya Alhamis, na gargadi da shawartar mutane daidaiku da rukunnai da su dakatar da gine-gine a filayen Gwamnati.

Yace abin da zababben gwamnan yayi wuce makad’i ne da rawa na bayar da umarni akan kudurin da ya shafi gwamnnati, bayan kuma gwamna mai ci a yanzu bai kammala zangon sa ba.

Malam Muhammad Garba yace a bisa tsarin dokar kundin tsarin mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje shine gwamnan Kano har yanzu zuwa 29 ga watan Mayu kuma yana da ikon zartar da duk abinda yake bisa doka har zuwa washegarin ranar da zai bar Mulki.

Kwamishinan ya ce gwamnoni jihohi suna da ikon bayarwa da kuma rarraba filaye, kuma kowacce gwamnati tayi irin wannan, ciki kuwa har da gwamnatin da ta gabata wacce Abban ya yiwa aiki.

Muhammad Garba yace sanarwar da Abban ya fitar ta haifar da rudani a cikin al’umma, ya kuma shawarce shi da ya kauracewa cigaba da yin hakan.

A karshe ya bukaci dukkan mamallaka filayen da suka mallaka bisa ka’ida da su cigaba da gininsu, kar su ji wani dar ko shakka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: