An ci gaba da kai hare-hare Khartoum baban birnin ƙasar yayin da aka kai kari wani asibiti da wasu bankuna.

An kai hari bankunan da kuma asbiti tare da cigaba da lalata wurare muhimmai.
Dakarun RSF na ci gaba da kai hare-hare domin neman kwace iko da ƙasar.

Wani likita ya bayyanawa BBC cewar wasu mutane sun kutsa asibiti dauke da makamai a cikin dare.

Bangarori biyu ke faɗa a tsakani wanda a baya su ka yi kira da a tsagaita wuta domin samar da sulhu.
A halin yanzu bangare biyun na tattaunawar sulhu a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.
A halin da ake ciki bangarorin biyu na ikirarin shirinsu na karɓar sulhu domin tsagaita wuta.
Tuni Najeriya ta ce ta kwaso ɗaliban ta da ke karatu a kasar bayan da rikicin ya ci gaba da tsananta.