Rundunar ’yan sandan Jihar Osun ta kama wani boka mai suna Isiaka Ogunkoya bisa zargin sa da kashe wani fasto tare da yin tsafi da shi a lokacin da faston mai suna Kalejaye Ezekiel ya je wajensa neman maganin da zai ba shi karfin iko da nuna mu’ujiza.



Bayan kama bokan a hanyarsa ta zuwa yankin Isoyin, bokan mai shekara 48 ya yi ikirarin aikata ta’asar tasa.
An kama bokan tare da wasu sassan jikin dan Adam wadanda ya ce na faston ne da ya je wajensa neman maganin da zai rika nuna mu’ujiza.
Jami’an ‘yan sandan sun kama bokan ne akan hanyarsa ta zuwa yankin Isoyin da ke Jihar.
Bayan kama bokan mai shekaru 48 ya amsa laifin da ake tuhumarsa dashi na aikata kisan.
A yayin kama boka an kama shine tare da wasu sassan jikin dan Adam wadanda ya ce na faston ne da ya je wajensa neman maganin da zai rika nuna mu’ujiza.
Matsafin ya bayyana cewa a lokacin da Fasto ya je gurinsa a lokacin ya na bukatar sassan jikin dan Adam domin yin tsafi.
Bokan ya kara da cewa Faston ya shaida masa cewa ya na son karin mu’ujizoji ta yadda zai kara samun mabiya a cocinsa.
Wanda hakan ya sanya ya samu damar yin amfani da faston gurin yin tsafin dashi a lokacin.
Matsafin ya ce da zuwan limamim majami’ar gurinsa ya ba shi wani jikon magani ya sha inda barci ya dauke shi wanda hakan ya bashi damar yanka shi tare da cire zuciyarsa kuma yayi amfani da ita wajen hada wani magani.