Connect with us

Labaran ƙetare

Wakilan Ƙasashen Duniya A Fannin Tsaron Sun Kammala Taron Don Shawo Kan Rikicin Ukraine

Published

on

Wakilan kasashen duniya sun yi wani taro na duba hanyoyin kawo karshen rikicin da ke faruwa a Kasar Ukraine.

Masu bayar da shawara kan harkokin tsaro na ƙasashen da kungiyoyin duniya sun kammala taron tattaunawa a Jeddah dangane da abubuwan da ke faruwa a kasar Ukraine.

A ranar Asabar 5th ga watan Agusta wanda aka yi na kasashen duniya 40 da kuma wasu kungiyoyin duniya ne su ka halarta.

Wakilai a zauren Majalisar Dinkin Duniya sunhalarci taron.

Zaman ya gudana ne karkashin jagorancin karamin minista sannan mai bayar da shawara kan harkokin tsaro Dakta Mosaad Bin Mohammad Al-Aiban.

ki

Wadanda su ka halarci taron sun yabawa kasar Saudiyya bisa gayyato mutane sannan ta shirya tare da tsara taron a cikin kasar.

Taron na zuwa ne a wani bangare na sake daura damara tare da cigaba da kuma ƙara kaimi wanda yarima Mohammad Bin Salman Bin Abdulaziz ya aiwatar, kuma masarautar saudiyya ta shiga tsakani tun a watan Maris na shekarar 2022.

Kasashe da kungiyoyin da su ka aike da wakilcin sun hada da, Argentine Australia, Bahrain, Brazil, Bulgaria, Canada Chile, da kuma ƙasar China.

Sauran su ne hadaddiyar daular Comoros, Czech, Denmark, Egypt, Estonia, European Commission, European Council, Finland, Germany, French Republic, India, Indonesia, Japan, Hashemite, Jordan Latvia da kuma Qatar, Korea, South Africa, Lithuania.

Haka kuma akwai Italian, Kuwait, Netherlands, Norway, Poland, Korea, Romania, Turkey, Hadaddiyar daular larabawa, Amuruka, majalisar dinkin duniya da kuma kasar Ukraine.

Mahalarta taron sun gamsu da cigaba da tattaunawa tare da bayyana ra’ayi, domin samar da hanyoyin na dorewar zaman lafiya.

Sannan sun gamsu da yadda aka samar da cigaba a zaman da ya gabata.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran ƙetare

Shugaban Ƙasar Madagaska Andry Rajoelina Ya Lashe Zaɓe A Karo Na Biyu

Published

on

Shugaban ƙasar Madagaska Andry Rajoelina ya sake lashe zaɓe karo na biyu, duk da kuwa ƙauracewa yin zaɓen da ƴan tsagin masu hamayya suka yi a yankin kudu maso Gabashin ƙasar ta tsuburin Afirka.

Andry ya samu kaso 58.95 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, wanda hukumar zaben ƙasar ta sanar a yau Asabar.

Ƴan takarkarun tsagin hamayya Siteny Randrianasoloniaiko da Marc Ravalomanana sun samu kashi 14.4 da kuma kashi 12. 1 kowannensu.

Ƴan takarkarun tsagin hamayya su goma sun yi kira ga magoya bayansu da su ƙauracewa yin zaɓen, duk da kuwa an sanya sunayensu a jikin takardar ƙuri’ar zaben da aka riga aka buga.

Hukumar zaɓen ta ce kaso 46 cikin 100 sun fito kaɗa ƙuri’a, amman ba a ga fuskar ko ɗaya daga cikin ƴan takarkarun hamayya 12 a wajen sanar da sakamakon zaɓen ba ranar da safiyar yau Asabar.

Ƴan siyasar tsagin hamayyar sun zargi shugaba Rajoelina da ƙoƙarin cigaba da mulki ta hanyar da bata dace ba, sun zargi shugaban da bai’wa kotuna da jami’an hukumar zaben cin hanci.

Continue Reading

Labaran ƙetare

Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Awanni Huɗu Kullum A Arewacin Gaza

Published

on

Ƙasar Isra’ila ta amince a tsagaita wuta na awanni huɗu a kullum a arewacin Gaza, don a bai’wa fararen hula damar ficewa daga yankin.

Fadar gwamnatin Amurka ce ta sanar da hakan a yau Alhamis, duk da cewa shugaban ƙasar Joe Biden ya ce babu cikakkiyar tsagaita wuta.

Biden ya yabawa Fara-ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bisa ɗan dogon hutu a faɗan, bayan tsawon wata daya da aka ɗauka ana fafata rikicin.

Sojojin Hamas da Isra’ila yanzu kowanne yana maɓoyarsa, kusa da inda ake gwabza faɗan a birnin Gaza, a yankin arewacin Zirin Gaza.

Mai magana da yawun sashin tsaron ƙasar  John Kirby ya sanar da manema labarai cewa, Isra’ila za ta fara Ƙaddamar da Dakatar da faɗan na awanni huɗu a kullum a yankin na Arewacin na Gaza.

“Isra’ilawa sun sanar da mu cewa, ba za a samu aikin sojin su a yankin ba na tsawon lokutan da aka ɗauka, kuma hakan zai fara daga yau.”

Continue Reading

Labaran ƙetare

An Sake Cafke Tsohon Shugaban Ƙasar Gini Bayan Ya Tsere Daga Gidan Yari

Published

on

An sake cafke tsohon shugaban gwamnatin soji ta ƙasar Gini Moussa Dadis Camara a jiya Asabar, bayan ya tsere daga babban gidan yari a Conakry babban birnin ƙasar.

Shugaban sojojin ƙasar ta Gini Ibrahima Sory Bangoura ya tabbatar da hakan, ya kuma ce Camara yana cikin ƙoshin lafiya, kuma an mayar da shi gidan yarin na Conakry.

Ya kuma ce an kuma cafke mutane biyu da suka tsere tare da shi, wato Moussa Tiegboro Camara da Blaise Gomou. Kuma an mayar da su gidan yarin su ma.

Sannan sojojin sun bayyana cewa, ana ta ƙoƙari don ganin an kamo ragowar ɗayan da suka tsere tare, wato Claude Pivi.

Kotun ɗaukaka ƙara a ƙasar wacce ta ke a Conakry, ta bayar da umarnin a yi cajin su da babban laifi dukka su huɗun.

Moussa Camara dai ya Ƙaddamar da juyin mulki a ƙasar, ranar 23 ga watan Disambar shekerar 2008. Wanda kuma ya zama shugaban gwamnatin sojojin ƙasar.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: