Kamfanin sarrafa siminti na BUA mallakin Abdulsamad Isiyaka Rabiu, ya sanar da rage farashin buhun siminti dan samun sauki ga ‘yan Najeriya.

A sanarwar da mahukuntan kamfanin suka fitar da yammacin yau Lahadi a shafin kafar sadarwar zamani na Facebook, sanarwar tana dauke da tabbacin rage farashin.
Sanarwar ta bayyana cewa, daga ranar Litinin 2 ga watan Oktoban da muke ciki, za a dinga siyar da simintin a kan Naira 3500 kowanne buhu a maimakon Naira 5000 da ake siyar da shi a baya.

Sun kara da cewa, yanzu haka ana gab da kammala aikin sabuwar masana’antarsu, wacce zata kara yawan simintin da suke sarrafawa zuwa tan miliyan 17 a duk shekara.

A karshen sanarwar kamfanin yace, dukkan wasu kaya da aka yi odarsu a tsohon farashin kuma ba a kai su ba, suma za a bayar da su ne akan sabon farashin da kamfanin ya ambata.