Rukunan matasa a sassa daban-daban na arewacin Najeriya, sun yi shakulatin bangaro da bikin murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kan Najeriya.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kasa Najeriya ta yi bikin murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, a jiya Lahadi 1 ga watan Oktoban shekara ta 2023.

A lokacin da ake tsaka da bikin murnar a sassan Najeriya, fusatattun matasa sun fito kan tituna da kuma shafukan sada zumunta, don nuna bacin ransu game da kashe-kashe, sace mutane, da kuma sauran manyan laifukan ‘yan ta’addah a yankin Arewacin Najeriya.

Sun kuma yi Allah wadai ga gwamnatin tarayya bisa gazawarta na ceto dalibai mata da aka yi garkuwa da su a jam’iar gwamnatin tarayya ta Gusau da ke Zamfara, ‘yan makonni bayan sace su.

Wakilin jaidar Daily Nigerian ya ruwaito cewa matasan sun sanya riguna dauke da tambarin #A_kawo_karshen_rashin_tsaro a arewa, da kuma hotunan #A_dawo_da_matan jami’ar Gusau, a duba rayuwar ‘yan arewa, jini yana kwarara a arewa da sauransu.

Sannan matasan kuma sun yi watsi da Allah wadai da jawabin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da aka yada, akan bikin na murnar ranar ‘yancin kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: