Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana hukuncin kotun ƙolin Najeriya aka shari’ar zaɓen shugaban ƙasa da cewa, sauƙi ne ga shugaba Tinubu da kuma ƴan Najeriya.

Shugaban ya faɗi hakan ne cikin wani rubutu da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya wallafa a shafin kafar sadarwa na X a yau Alhamis.
Idan za a tuna a yau ne dai kotun ƙolin Najeriya ta kori ƙarar da ƴan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar na jam’yyar PDP da Peter Obi na jam’yyar LP su ka shigar gabanta. Su na ƙalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2023 da ya gudana ranar 25 ga watan Fabarairu.

A jawabin da Garba Shehu ya wallafa ya ce tsohon shugaban Buhari ya maimaita abinda ya faɗa akan hukuncin kotun sauraron ƙarar zaɓe ranar 6 ga watan Satumba. Inda ta tabbatar da nasarar ta shugaba Tinubu.

Inda ya ce hukuncin abun maraba ne na tabbatar da ƙudirin mafi yawan ƴan Najeriya, akan ƙudirin wasu tsiraru.
Ya kuma bayyana cewa shari’ar da aka shafe watanni takwas ana fafatawa ta zo Ƙarshe, sai masu ƙorafi su rungumi ƙaddara don iya damar da kundin tsarin mulki ya basu kenan ta zuwa kotun ƙoli.
Ya ce lokaci ne yanzu da zasu bar waɗanda aka zaɓa su yi mulkinsu ga al’umma don su ji daɗinsa, su cika alkawarin da jami’yyar APC ta yi wa ƴan Najeriya.
A Ƙarshe Muhammadu Buhari ya yiwa shugaba Tinubu fatan alheri tare da muƙarraban gwamnatinsa, a tsawon lokacin da zasu ɗauka su na Mulki.